Al’umar karamar hukumar Kafur ta Jihar Katsina sun tafka asarar miliyoyin nairori a gonaki sakamakon mamakon ruwa sama da Kankara da aka tafka a Jihar.

Shugaban karamar hukumar Kafur Garba Kanya ne ya tabbatar da hakan.
Shugaban ya ce mamakon ruwan ya haifar da a sarar gonaki akalla 300 tare da lalacewar ginin gidaje masu tarin yawa a Jihar.

Garba Kanya ya kara da cewa manoma na daf da su fara girbe amfanin gonakinna su aka tafka ruwan saman da Kankara a kauyen.

Shugaban ya ce asarar ta shafi gonakin Masara Shinkafa Barkono Waken suya Gero da kuma Albasa.
Kanya ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin sun shaidawa hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar da hukumar raya Karkara da kuma sauran wasu hukumomin domin kididdige asarar da aka tafka.
Malam Abdullahi Gozaki wani mazaunin kauyen Gozaki ya bayyana cewa ba a taba yi musu ruwan sama da Kankara irin wanda aka yi musu ba.
Malam Abdullahi ya kara da cewa ba a dade da fara yin ruwan ba aka samu asarar tare cirewar rufin gidajen al’umar yankin harta kai ga ya fasa gilasan motocin mutane.
Abdullahi Gozaki ya ce lamarin ya faru a unguwannin Gozaki Kanya Dutsen kura Gidan Sabo Gidan Danwada unguwar Fulani unguwar Wanzamai Unguwar Tsamiya unguwar Kabalawa unguwar Dandabo da kuma unguwar mai girma.