Majalisar tsaro a Najeriya na shirin samar da rundunar tsaron haɗin gwiwa domin ƙarfafa daƙile ayyukan shigo da haramtattun kayayyaki.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya shaida hakan yau Alhamis yayin ganawa da manema labatai a Abuja.

Sabuwar dokar da aka aikewa masana a harkokin tsaro da kuma majalisar dokokin Najeriya domin nazarinta.

Ministan ya ce manyan jami’an tsaro su nuna gamsuwa da sabuwar dokar wadda za ta karfafa dokar hana shigar da haramtattun kayayyaki ƙasar.

Sabuwar dokar da za a yi haɗin gwiwar jami’an tsaron za ta mayar da hankali ne wajen daƙile shigo da makamai, satar danyen mai, sinadarin hada makamai, harsashi, da sauran haramtattun kayayyaki.

Ya ce manufar hakan shi ne dakile dukkan hanyoyin ta’addanci a ƙasar zuwa watan Disamban shekarar da mu ke ciki.

A zaman majalisar tsaro na yau, dukkan shugabannin tsaro a Najeriya sun nuna goyon bayansu a kan tsarin samar da NATFORCE.

Leave a Reply

%d bloggers like this: