Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta tabbatar da kama mutane 761 wadanda ta ke zargi da yin safarar miyagun kwayoyi tare da kwace kilogiram 11,000 na gurbatattun magunguna a Jihar Kaduna.

Shugaban hukumar na Jihar Mista Umar Adoro ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin Labaran Najeriya a Jihar a ranar Alhamis.

Adoro ya ce sun kama mutanen ne watannin takwas da su ka wuce na farkon shekarar 2022 da mu ke ciki.

Mista Adoro ya kara da cewa mutane 610 daga cikin wadanda aka kama masu shan miyagun kwayoyi ne inda hukumar ta tsare 480 daga cikin su domin kawar da su daga shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Shugaban ya ce 151 daga cikin su na hannun su 69 kuma su na hannun jami’an tsaro yayin da 82 su ke gaban kotu domin yi musu hukunci.

Adoro ya ce daga cikin kayayyakin da su ka kama ciki harda tabar wiwi da wasu magunguna da su ke sanya maye.

Sannan ya bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da bincike domin kawo karshe masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin Jihar.

Adoro ya kuma yi kira ga mazauna Jihar da su ba su hadin kai domin ganin an dakile faruwar hakan a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: