Ministan shari’a a Najeriya Abubakar Malamai SAN ya yabawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wajen kawo ci gaba a ɓangaren shari’a.

Malami ya bayyana jinjina ga gwamna Ganduje yayin wata liyafar girmamawa da aka shirya masa da wasu manyan mukarrabai a bangaren shari’a a Najeriya.
Ministan ya tabbatar da cewar gwamna Ganduje ya kawo gyara da ci gaba mai yawan gaske wanda ya zama abin koyi ga sauran gwamnoni.

Sannan ya ce Ganduje ya taimakawa gwamnatin tarayya wajen bin tsarin yaƙi da cin hanci da rashawa wanda hakan ya samar da gagarumar nasara.

A wata sanarwa da Malam Abba Anwar, babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce ministan ya yabawa gwamna Ganduje ganin yadda ya samar da ayyukan ci gaba a gwamnatinsa wanda hakan ya sanya jihar Kano ta zamto a sahun gaba cikin jerin jihohin Najeriya a ɓangaren ayyyukan raya ƙasa.
Yayin da ya ke nasa jawabin, a taron liyafar da aka shirya a gidana gwamnatin Kano, gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta kafa wani kwamiti na musamman wamda zai dinga duba a bangaren shari’a tare da kawo hanyoyin ci gaba ta yadda za a ci gaba da kawo sauyi mai ma’ana a ɓangaren.
Sannan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen ganin ɓangaren shari’a a jihar na yin gogayya da sauran ɓangaren shari’a na duniya tare da tafiya da zamani.