Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ta ware naira biliyan 1.5 domin magance matsalar rashin tsaro da Jihar ke fuskanta.

Gwamnan Jihar Aminu Masari ne ya tabbatar da hakan a wajen bikin yaye jami’an tsaron sa-kai 600 wanda ya gudana a kwalejin hukumar tsaro ta fararen hila wato NSCDC da ke Jihar a ranar Asabar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnantin Jihar Alhaji Muntari Lawal ya yabawa jami’an sa-kai akan namijin kokarin su wajen tallafa wa jami’an tsaro a Jihar.

Alhaji Lawal ya kara da cewa ‘yan sa-kan sun bayyana cewa za su yi aiki tukuru tare da jami’an tsaro wajen shiga lungu da sako domin bincike masu aikata ta’addanci musamman masu garkuwa da mutane fashi da makami da sauran wasu laifukan.

Sakataren ya kara da cewa gwamnatin Jihar ta na tallafawa hukumomin tsaro da kungiyoyi da wadanda su ka sadaukar da kansu domin Jihar ta magance matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar.

A yayin jawabin mai bai wa gwamnan shawara kan sha’anin tsaro Alhaji Ibrahin Katsina ya bayyana cewa daga cikin jami’an tsaron sa-kan 600 sun kasance maza da mata wanda su ka yi karatu a bangare da dama cikin harda masu digiri.

Kwamandan kwalejin hukumar ta NSCDC Babangida Abdullahi ya ce an horar da jami’an tsaron na sa-kai na tsawon makonni biyu akan yadda za su yi amfani da makamai da sauran wasu hanyoyin da za su bi domin magance matsalar rashin tsaro a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: