Kakakin majalisar wakilai a Najeriya Femi Gbajabiamila ya aike wa ministan ilimi da ƙungiyar ASUU takardar gayyata domin ganawa da su a gobe Talata.

Majalisar ta dauki matakin ganawa da ƙungiyar malaman jami’a da ministan ilimi sakamakon yajin aikin da aka shafe watanni bakwai su na yi.
Takardar gayyatar da aka aikewa kungiyar an bukaci shugabanci da sauran masu ruwa da tsaki su hallara a zauren majalisar gobe domin kawo karshen yajin aikin.

Takardar gayyatar ta nuna yadda ƙungiyar ta nuna damuwarta a dangane da zaman dalibai a gida a sakamakon rashin karatu da ba a yi a mafi yawan jami’a a Najeriya.

Majalisar ta roƙi shugabancin malaman jami’a ASUU da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana a gabanta domin kawo karshen matsalar baki daya.
Sannan majalisar ta bukaci ƙungiyar ta zo da bukatunta a rubuce ta yadda komai zai zo karshe daga gobe Talata.