Manoma a jihar Taraba sun nuna damuwarsu a kan yadda ambaliyar ruwa ta shafe gonakinsu.
Fiye da kashi 90 na amfanin gonakin da su ke yankin iyaka da jihar Adamawa ne su ka lalace a sanadin ambaliyar ruwan sama a bana.
Ƙananan hukumomin da su ka shafa akwai Gassol, Lau, Ibbi, Ardo Kola, da ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo.
Wani manomi mai suna Adamu Sa’idu ya shaidawa jaridar daily trust cewar, fiye da kashi 80 na amfanin gonarsa ya lalace a sanadin ambaliyar ruwan sama.
Wasu daga cikin manoman sun nuna damuwa ganin yadda su ka karɓi bashi domin yin noma a bana amma ambaliyar ruwan ta lalata amfanin gonar.
Shugaban manoma shinkafa a jihar Taraba Tanko Andami ya ce ƙungiyar ta fara tantance mutanen da su ka yi asara a sanadin ambaliyar ruwan.