Jami’an tsaron soji da yan sanda sun hana ɗalibai gudanar da zanga-zanga a Kaduna.

Fusatattun ɗaliban sun ɗauki matakin yin zanga-zanga tare da toshe wasu manyan hanyoyi don ganin an kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a su ke yi.

A ranar Talata kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya gargaɗi ɗaliban don ganin ba su toahe kowacce hanya a jihar ba.

An aike da jami’an soji da yan sanda da ƴan sa kai babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja domin ganin ɗaliban ba su toshe hanyar ba a yau.

Sai dai shugaban ɗalibai a jihar ya ce ba za su toahe kowacce hanya ba don kada su wahalar da jama’a musamman masu zirga-zirga a hanyar.

Al’amarin yajin aiki na daɗa zafafa yayin da gwamnati ta kai ƙarar malaman jami’a su kuwa daliban su ka ɗauki matakin zanga-zanga duka domin ganin an kawo ƙarshen yajin aikin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: