Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da kama wasu mutane biyu wadanda ake zargin su da bude makarantar kwakejin koyar da aikin lafiya ta bogi a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Wasiu Abiodum ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Talata a Minna babban birnin Jihar.
Kakakin ya ce an kama mutanen ne a cikin karamar hukumar Basso ta Jihar.

Wasiu Abiodum ya bayyana cewa mutanen da ke matsayin shugaba da mataimakin sa sun sanyawa makarantar da su ka bude suna Excellence College Of Health.

Kakakin ya kara da cewa kafin rufe kwalejin makarantar ta na dauke da dalibai 100 inda kowanne dalibi ya ke biyan nairan 78,000 a kowacce shekara.
Abiodum ya ce sun kama mutanen ne da taimakon bayanan sirri da su ka samu akansu a ranar 9 ga watan Satumban da mu ke ciki.
Kakakin ya kara da cewa mutanen sun shaida musu cewa sun bude makarantar ne a shekarar 2020 daga bisani kuma su ka fara daukar dalibai a shekarar 2021 ba tare da sun nemi izinin kowacce hukuma ba a fadin Najeriya.
Abiodum ya ce mutanen sun tabbatar musu da cewa su na nunawa mutane takardun bogi domin mutane su samu damar shiga.
Wasiu Abiodum ya bayyana cewa daya daga cikin mutane biyun da aka kama wanda shine matsayin daraktan makarantar dan asalin garin Enugu ne, kuma su ka dauki malamai 20 domin yi musu aiki.
Kakakin ya ce da zarar sun kamma bincike za su gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci.