Shugaban ƙungiyar a kan kare muradin al’umma da ci gabansu Dakta Onyekachi Ubani zai kai gwamnatin tarayya ƙara a kan matakin dokar da ake ƙokarin samarwa na hana cin ganda a ƙasar.

Hakan ya biyo bayan furucin daraktan cibiyar bincike a kan fatun dabbobi na Najeriya ya yi na ƙoƙarin mika bukatar hana cin ganda a Najeriya.

Lauyan ya ce babu abu mafi sauƙi da ƴan Najeriya su ke iya siya wanda ya ke da sinadarin gina jiki da ya wuce ganda kuma hakan tauye haƙƙin jama’a ne.

Lauyan ya nuna damuwarsa a kan yunƙurin da ake yi na yin dokar hana sarrafa fatar dabbobi zuwa nama da mutane su ke ci wanda ake kira da ganda ko kuma Ponmo.

Lauyan ya zargi shugabannin Najeriya da tauye duk wata kafa da ƴan ƙasar ke jin sauƙi a rayuwarsu.

Hukumar bincike da kimiyya da fasaha a kan fatun dabbobi ce ta sanar da gabatarwa majalisar dokoki ƙudiri na yin dokar da za a haramtawa ƴan ƙasar cin fatun dabbobi.

Matakin da hukumar ta ɗauka ta yi ne da nufin farfaɗo da kamfanonin sarrafa fatun dabbobi tare da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: