Mutane uku sun rasa rayuwarsu yayin da aka ceto wasu huɗu a raye a sanadin kifewar wani kwale-kwale a Abuja.

Al’amarin ya faru a ƙauyen Chakumi da ke ƙaramar hukumar Abaji ta babban birnin tarayya Abuja.
Mai unguwar Chakumi Mohammad Magaji ya tabbbatar da cewar masunta sun ceto mutane huɗu a raye kuma an yi gaggawar kai su asibiti.

Kifewar jirgin ruwan ya faru a ranar Laraba sai dai har yanzu ba a gano sauran mutane biyu ba.

Waɗanda su ka jikkata an kai su asibitin Dobi da ke Gwagwalada a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewar mutanen da aka ceto sun dira daga cikin kwale-kwalen yayin da ya ke ƙoƙarin kifewa.
Sannan daga cikin waɗanda su ka mutu akwai wata matar aure.