Kwamishinan ilmi na Jihar Farfesa Badamasi Lawal ya bayyana cewa dalibai mata sun fi maza kokari a yayin jarrabawar kammala makarantar Sakandire wadda daliban su ka rubuta a shekarar 2021 da ta gabata.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wajen taron rufe shirin bai wa dalibai mata ilmi GEP III wanda aka gudanar a Jihar.

Farfesa Badamasi ya ce kwazon na dalibai ya samo asali ne sakamakon jajircewar da gwamnatin Jihar ta yi na inganta ilmin ‘ya’ya mata ta hanyoyi daban-daban na bai wa daliban ilmi.

Kwamishinan ya bayyana cewa a shekarar ta 2021 dalibai 18,321 su ka rubuta jarrabawar ta WASSCE a dukkan fadin Jihar wanda gwamnatin Jihar ta dauki nauyin su.

Farfesa Badamasi ya kara da cewa dalibai maza 10,441 ne su ka rubuta jarrabawar yayin da mata 7,880 su ma su ka rubuta jarrabaar.

Badamasi Lawal ya ce sakamakon jarrabawar ya bayyana mafi yawan dalibai 4,627 mata ne su ka samu nasara a harshen Turanci wanda ya kai kashi 58.7 cikin 100.

Kwamishinan ya ce daga cikin dalibai maza 10,441 5,632 ne su ka samu nasara a harshen Turanci wanda ya kasan ce kashe 54 cikin 100 inda ya ce sakamakon ya nuna dalibai mata sun fi maza kokari a harshen na Turanci.

Farfesa Lawal ya bayyana cewa a bangaren darasin lissafi kuwa matan sun sake zarce mazan inda mata 5,678 su ka samu nasara yayin da maza 4,726 su ka samu makin da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: