Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da kashe mutane 38 waɗanda ake zargi mayaƙan ƙungiyar ISWAP da Boko Haram ne.

An kashe mayaƙan yayin luguden wutar da jami’an su ka shafe makonni biyu su na yi a dajin Sambisa.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar Manjo Janar Musa Ɗanmadami ne ya tabbatar da haka yayin ƙarin haske ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Jami’an sun kashe mayaƙan ta hanyar kwanton ɓauna a garuruwa yankunan Kukawa, Monguno, Kaga, Dikwa, Biyu, Damboa, Gwoza, Mafa, Konduga, Bama da ƙaramar hukumar Guzamala.

Jami’an sun kuɓutar da mutane 130 sannan sin kama wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne su 46 sai mutane 12 da ake zargi su na kai wa mayaƙan Boko Haram da ISWAP makamai.
Haka kuma jami’an sun ƙwato makamai masu yawa daga hannun mayaƙa. daga ciki akwai bindigu ƙirar AK47 da harsasi mai yawa sai kekuna, babura da wayoyin hannu.