Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan halartar taron majalisar ɗinkin duniya a birnin New York.

Shugaba Buhari ya halarci babban taron majalisar ɗinkin duniya kashi na 77 kuma shi ne taron da zai halarta na ƙarshe a matsayinsa na shugaban ƙasa.
A ranar Larabar makon da ya gabata shugaban ya gabatar da jawabi a zauren majalisar ɗinkin duniya inda ya bayyana cewar wannan ne karo na ƙarshe da zai halarci taron a matsayinsa na shugaban Najeriya.

Shugaban ya sauka a filin jirgin sama na Abuja kuma ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya da ministan Abuja.

A taron da ya halarta, shugaban ya bukaci a yafewa ƙasashe matalauta basukan da ake binsu.
Sannan ya jaddada ƙafafaf alaƙarsa da wasu ƙasashen turai domin kawo cigaba a Najeriya.