Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin shiga tsakanin addinai a jihar.

Hakan na ƙunahe a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano ya fitar, sanarwar ta ce kwamitin zai yi aiki ne tare da wakiltar jihar a babban taron da za a yi na ƙasa.

Kwamitin mai mutane 23 daga ɓangaren addinin musulunci da kirista.

Samar da kwamitin wanda zai taimaka wajen wayar da kai, tare da samar da fahimta da kuma kare martabar addinai.

An ƙaddanar da kwamitin a ɗakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin Kano.

Gwamnan ya yi hakan ne da nufin mutunta addinai a wani salo na wanzar da zaman lafiya a jihar Kano.

Kwamitin wanda Sheik Muhammad Bin Uthman ya ke jagoranta tare da mataimakinsa Arch. Bishop Peter ke yi masa mataimaki sai kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano wanda shi ne sakataren kwamitin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: