Yayin da ya rage kwanaki biyu a buɗe takunkumi tallan ƴan takara a Najeriya,hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta gargaɗi ƴan siyasa a kan kalaman tunzuri.

A ranar Laraba ake sa ran ɗage takunkumin tallan ƴan takara da yaɗa manufa yayin da ya rage ƙasa da watanni bakwai a gudanar da zaɓen shekarar 2023.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya yi gargaɗin yau Litinin a Abuja.

Shugaban ya ce wajibi ne ƴan siyasa su kiyaye kalaman tunzuri ko ɓatamci ga takwarorinsu ƴan takara na wasu jam’iyyun.

Yayin da ya ke jawabin a wajen taron ƙarawa juna sani da hukumar ta shirya a kan abubuwa masu hatsari a kan zaben 2023, shugaban hukumar wanda kwamishinan hukumar na ƙasa Fetsu Okoye ya wakilta, ya ce za a ɗage takunkumin tallan ƴan takara a ranar Laraba.
Ya ce dokar da hukumar ta samar ta wajaba kare mutuncin kowa a ɓangaren al’ada, addini, tare da tabbatar da cewar an tsare lafiya da rayuwar kowa.
A galin da ake ciki kwanaki 152 ne su ka rage a gudanar da babban zaɓen shekarar 2023.