Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta gargaɗi ‘yan ƙasar da su ke amfani da man da ya ke sauya launin fata.

Babbar darakta a hukumar Farfesa
Mojisola Adeyeye ita ce ta bayyana hakan a wani taron kwana biyu da hukumar ta shirya a Jihar Legas a jiya Lahadi.

Daraktar ta kara da cewa sinadaren da ake hada Man da ya ke kwale fata ya na dauke da abubuwan da su ke sanya cutar daji a cikin fatar dan Adam tare da lalata gabobi har ma ka iya kaiwa ga mutuwa.

Adeyeye ta ce ba sun haramta shafa Man ba ne saboda kwaila fata sun haramta shi ne sakamakon sinadaren da ake hadawa da shi kuma ka iya haifar da Ciwon Koda da ciwon Hanta harma da ciwon daji a jikin al’umma.

Daraktar ta kara da cewa mafi akasarin Man ana shiga da shi ne ta barauniyar hanya ba tare da sanin hukumar NAFDAC ba.

Mojisola ta ce irin wadannan kayayyakin sun zama annoba a tsakanin maza da mata mazauna Najeriya wanda kuma hakan babban abin damuwa ce.

Hukumar ta kuma bayyana cewa masu harkar kwalliya da gyaran jiki na taka muhimmiyar rawa wajen amfani da kayan tare da hada su da Karas da Gwanda da sauran kayan ita tuwa da sunan gyara fata.

Daraktar ta bayyana cewa ana cutar mutane ne a na sayar musu da sunan gyara fata musamman a shafukan sada zumunta.

Ta ce wasu ma su na hada kai da wasu jami’an lafiya domin su tallafa musu wajen sayar da kayan.

Mojisola ta ce masu irin wannan mummunar mummunar akidar su na yi ne aboye wanda kuma hakan zai bai wa hukumar matukar wahala wajen gano wadanda su ke sayar da irin wadannan kayayyakin a shaguna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: