Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane uku tare da yin garkuwa da mutanen 22 a wasu kauyuka da ke cikin karamar hukumar birnin gwari ta Jihar Kaduna.

‘Yan bindigan sun yi aika-aikar ne a yammacin ranar Asabar a kauyen Hayin gada da ke Damari inda su ka hallaka mutane biyu sannan su ka yi garkuwa da wasu 12 tare da kwashe kayayyakin sayarwa na wasu shaguna.
Shugaban hukumar cigaban mutanen birnin gwari BEPU Ishaq Usman Kasai shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a safiyar yau Litinin.

Shugaban ya ce a ranar Asabar maharan sun hallaka mutum daya tare da yin garkuwa da shida a yankin Farm Cetre da ke kan hanyar Kaduna zuwa birnin gwari.

Usman Kasai ya kara da cewa har ila yau ‘yan bindigan sun sake yin garkuwa da mutane hudu a dajin Jangali sannan su ka sake yin garkuwa da manoma da Babura uku a yankin Kamfanin Doka duk da a Jihar.
Shugaban ya ce ba za su taba gajiyawa wajen kiraye-kiraye da hukumomin tsaro domin su kara kaimi wajen yakar ‘yan bindiga da su ka addabi yankunansu.