Rundunar ƴan sanda a Katsina sun tabbbatar da kisan wani jami’insu mai suna Idris Musa a babbar hanyar Katsina zuwa Jibia.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Gambo Isah ne ya shaidawa yan jarida hakan, ya ce wasu da ake zargi yan bindiga ne su ka kashe jami’in tare da ƙone abin hawansa.
Al’amarin ya faru a ranar Litinin, a yankin Maƙera garin da ke kusa da babban birnin Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya sake tabbatar da cewa a kan babbar hanyar ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya waɗanda ba a kai ga gani adadinsu ba.

Ya ce mutanen da aka yi garkuwa da su ƴan kasuwa ne da ke yin kasuwancinsu tsakanin Jibia zuwa cikin garin Katsina.
Wani da lamarin ya faru a gabansa ya ce ƴan bindigan sun toshe hanyar ne a a ranar Litinin da misalin ƙarfe 08:00am na safe.