Dakarun rundunar sojin Najeriya sun bazama neman ƴan bindigan da su ka kai wa jami’an soji hari a jihar Anambra.

A na zargin sojoji biyar ne su ka rasa rayuwarsu a yayin da aka kai musu harin kwanton ɓauna a Umunze ta jihar Anambra.

Harin da aka kai jiya Laraba, a kusa da babbar kasuwar Nkwo babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

Duk da cewar ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra na da ƙarfi a jihar, amma ba su bayyana cewar su su ka kai hari kan sojojin ba.

Gwamnatin jihar ta yi Alla-wadai da faruwar hakan, tare da shan alwashin kamo waɗanda ake zargi don ganin sun fuskanci hukunci.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce nan da watan Disamban shekarar da mu ke ciki za ta tabbatar an kawo ƙarshen dukkan ta’addanci a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: