Majalisar wakilai a Najeriya ta ce akwai yuwuwar sake ɓarkewar annobar cutar Ebola a Najeriya.
Majalisar ta yi wannan bayani ne a yayin zaman da ta gudanar yau Alhamis a Abuja.
Guda cikin mambobin majalisar Dachung Bagos ne ya gabatar da ƙudirin a madadin sauran ƴan majalisar tare da kira ga gwamnati domin ganin ta ɗauki matakin gaggawa a kai.
Majalisar ta ce akwai alamu na fantsamar cutar Ebola a Najeriya sakamakon yadda ta ke ci gaba da yaɗuwa a wasu ƙasashen Afrika.
A cewar majalisar, Najeriya na iya fuskantar barazanar bazuwar cutar la’akari da yadda cutar ke yaɗuwa a ƙasar Sudan ga kuma ƙarancin riga-kafin ta.
Majalisar ta buƙaci hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya da su tabbatar sun saka idanu wajen tantance mutanen da ke shige da fice domin kiyaye faɗawa hatsarin cutar.
Sannan ta ce akwai buƙatar hukumar NCDC ta shirya ƙwarai domin ganin an yi wa tufkar hanci kafin bazuwarta a Najeriya.