Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC a Jihar Legas ta bayyana cewa ta samu nasarar kama Litar man fetur 21,000 daga wasu mutane da ake zargin barayin mai ne a Jihar.

Rahotannin sun bayyana cewa jami’an sashen yaki da satar mai na yankin Badagry ne su ka samu nasarar kama barayin a lokacin da su ke tsaka da sintiri a daren ranar Talata.
Hukumar ta ce a yayin sintirin sun kama jarakunan Man guda 720 wanda kowannensu ta ke dauke da lita 30 na Mai.

Rahotanni sun bayyana cewa ana kautata zaton mutanen za su fita da Man ne zuwa kasashen ketare.

Wasu majiyoyi daga Jihar sun bayyana cewa mutanen sun tsere a lokacin da jami’an na NSCDC su ka isa maboyarsu.
Jami’in shiyya na hukumar da ke Badagry CS Akinyemi Ayodeji ya bayyana cewa kimar man da aka kama ta kai naira Miliyan hudu.
Akinyemi ya ce za su aike da kayan zuwa hedkwatar Hukumar da ke Jihar don cigaba da bincike.
Shugaban hukumar na Jihar Eweka Okoro ya tabbatar da kama kayan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta bakin mai magana da yawunsa.
Sanarwar ta ce tuni su ka gano masu kayan kuma za su kamo mutanne nan ba da dadewa ba.