Wata babbar kotu da ke Jihar Benue ta bayar da izinin garkame wani mutum wanda yayi kokarin sayar da ‘yarsa akan kudi Naira Miliyan 20.

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar su ne wadanda su ka gurfanar da wanda ake zargin shi da abokinsa a gaban kotun.

Jami’an sun ce abokin nasa shine wanda ya taimaka masa wajen hadin baki domin a siyar da yarinyar da kuma safarar mutane.

Jami’ar ‘yar sanda mai gabatar da kara ta bayyana cewa an kama mutanen ne a lokacin da su ke kokarin sayar da yariyar mai shekara hudu.

Ta ce ana tsaka da cinikin yarinyar su ka kama mutanen yayin da mutumin da za su sayarwa da yariyar ya tsere.

Jami’ar ta kuma bukaci kotun da ta yanke musu hukuncin sakamakon karya wasu dokokin da su ka saba dokar Jihar.

Bayan gabatar da karar Alkaliyar kotun ta aike da su gidan yari zuwa ranar daya ga watan Disamba domin ci gaba da da shari’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: