Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da tsintar wani jajiri wanda ake kyautata zaton mahaifiyarsa ce ta jefar da shi a cikin Kwandon shara.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Benjamin Hundeyin ya ce an tsinci yaron da aka jefar ne a cikin Leda.

Kakakin wanda ya dora hoton jajirin a shafinsa na Twitter a jiya Alhamis ya ce ba don an yi gaggawar gano yaron ba da tuni ya rasa ransa.

Benjamin ya kara da cewa tun bayan tsintar yaron yana cikin koshin lafiya.

Kakakin ya yi kira ga mata masu dabi’ar zubar da ciki da su daina hakan don ya saɓa da dojar ƙasa.

Inda ya ce jefar da jajiran babban laifi ne kuma idan aka kama mutum zai fuskanci hukuncin mai tsanani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: