Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci al’ummar jihar su zamto jakadun zaman lafiya.

Gwamna Ganduje ya bayyana buƙatar hakan a cikin jawabinsa na zagayowar ranar samun ƴancin kai da ya gabatar a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar Ƙofar Mata a Kano.
Yayin da Najeriya ke cika shekaru 62 da samun yancin kai, gwamna Ganduje buƙaci jama’a su kauceea dukkan maganganu da ayyukan da za su iya rusa zaman lafiya a jihar Kano.

Gwamnan ya godewa mutanen Kano a bisa haɗin kai da su ka bayar tare da tabbatar musu da cewar a shekara mai zuwa wani gwamnan ne zai kasance a Kano ba shi ba.

Sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da haƙuri a kan kasancewar bambancin ɗabi’u addini da al’ada wanda jihar Kano da Najeriya ke da su.
A taron da aka gudanar, sarkin Kano Alhaji aminu Ado Bayero ya jagoranci addu’a ta musamman a kan zaman lafiya tare da buƙatar matasa da su zamto jakadun zaman lafiya a duk wajen da su ka sami kansu.