Wani matashi ya harbe kaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Karamar Hukumar Kaima ta Jihar Kwara.

Wadandan lamarin ya shafa dai ’ya’yan wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunkurin tabbatar da ingancinsa.
A cewar manema labarai lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin daji bayan mai aukuwar ta auku.

Da yake zantawa da manema labarai a yau Litinin, jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya bayar da umarnin a fara bincike a kan lamarin.

Okasanmi ya ce bayan sun daura maganin bindigar a jikinsu, sai babban cikinsu ya yi amfani da bindigar mahaifinsu ta farauta ya harbi kaninsa.
Sai dai an yi rashin sa’a maganin bai yi aiki ba, lamarin da ya sanya nan take kanin da aka harba ya mutu.
Okasanmi ya shawarci iyaye da subrika zuba idanu kan duk wani motsi na ’ya’yansu domin gudun faruwar mummunan lamari makamancin wannan.