Shugaban kasa mahammadu Buhari ya ce ya yi matukar farin ciki game da kubutar fasinjojin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna wadanda aka yi garkuwa da su a cikin jirgin a watan Maris.

Shugaban ya bayyana hakane ta bakin mai taimaka masa ta fanin yada labarai Malam Garba Shehu a jiya laraba.
Kuma ya gana da mutanen aka sako yau a Abuja.

Buhari ya ce ya na mai matukar jin dadi tare da farin ciki bisa wannan nasarar ta kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su tsawon lokaci.

Sannna ya ce ya na jinjinawa jamian tsaro bisa taka rawar da su kai wajen kubutar da wanda aka yi garkuwa da su tare sauran hukumomin tsaro.
Kuma ya taya iyalan wadanda aka yi garkuwa da su farin ciki ganini yadda suka sami iyalan su cikkin koshin lafiya ba tare da matsala ba.
Cikin sakon na shugaban ya bayyana cewa gwamanati za ta ci gaba da kara mai da hankali wajen tsare rayukan alumma tare da kawo karshen duk wata kungiyar ta’addanci a kasa baki daya.
Idan ba a manta ba an yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan jirgin Abuja zuwa Kaduna tun a watan maris din wannnan shekarar wadanda aka shiga cikin jirgin da suke aka yi awon gaba da su akalla su 50, saida sai dai tun lokacin yan garkuwa sun saki wasu daga ciki sannnan a jiya laraba suka saki sauran wadanda suka yi gurkuwa da su 23.