Hukumar ƴan sanda a jihar Jigawa sun ce mutum guda ya rasa ransa yayin da shanu bakwai su ka mutu a hatsarin mota a jihar.

Al’amarin ya faru a ƙaramar hukumar Gagarawa a ranar Talata.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Lawan Shiisu ya ce an ɗauki shanun da nufin kai su jihar Yobe lamarin ya rutsa da su.

Motar ta yi taho mu gama da babbar mota lamarin da ya haddasa asarar rayuwar mutum guda da kuma shanu bakwai.

A cewar jamj’in, an ɗakko shanun su 38 kuma hatsarin ya faru da ƙarfe biyu na rana.
Sannan akwai mutum tara da su ka jikkata kuma an kai su asibitin Gagarawa domin kula da lafiyarsu.
Sai dai ba su bayyana dalilin faruwar hatsarin ba.