Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba matsayin ranar hutu mauludi na murnar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a jawabin da Sakataren din-din-din na ma’aikatar, Shuaib Belgore ya fitar a madadinsa a ranar Alhamis.

Aregbesola ya shawarci yan Najeriya su yi koyi da dabi’un Annabi Muhammadu na soyayya, hakuri, ibadah don samar da zaman lafiya a doron kasa.

Aregbesola ya kwadaitar da yan Najeriya, musamman Musulmai, su kauracewa fadace-fadace, saba doka da kuma aikata laifuka.

Sannan yayi addu’a akan nemawa kasa zaman lafiya da kuma shuwagabanni na gari a zaben shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: