Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafshoshin sojin kasar Najeriya da su koma yankin Arewa Maso Gabas don taimaka wa nasarorin da dakarun soji suka samar na yakar ‘yan ta’adda a yankin.

Buhari ya bayar da wannan umarnin ne a makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Jihar Kaduna a taron yaye wa da kuma kaddamar da daukar sabbin dalibai.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce, ya umarci manyan hafshoshin sojin kasar da su tare a yankin Arewa Maso Gabas domin dora wa a kan nasarorin da aka samu na yakar ta’addanci a yankin.

Ya na kuma kira ga ‘yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaro na soji da sauran jami’an tsaro goyon baya domin a samu nasarar kawar da ta’addanci a daukacin fadin kasar.

Ya ce yin hakan na da muhimmanci matuka, musamman ganin yadda zaben 2023 na kara karatowa, kuma ya yi alkawarin tabbatar da an gudanar da zabubbuka cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin kuma ingantaccen zabe.

Shugaba Buhari ya kuma zayyano wasu daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a shekaru bakwai, inda ya danganta ayyukan a matsayin wadanda suka fi na wanda mulki kasar a shekaru 38 da suka wuce.

Ya kuma taya daliban da aka yaye murna, inda ya ce, a yanzu ne suka bude sabon shafi a gidan soji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: