Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta gayyaci ƴan sanda shida zuwa shelkwatarta da ke Ikeja bisa zargin karɓar naira dubu 100 daga hannun wani mutum.

Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Juma’a.

Yan sanda shida ne ke da hannu a lamarin. An gayyace su shelkwatar da ke Ikeja domin yi musu tambayoyi.

A jiya Alhamis ne dai wani mai suna Oluwagbadura, a shafin sa na Twitter, ya wallafa zargin cewa wasu ƴan sanda sun kwace masa kuɗi.

Ya yi ikirarin cewa da misalin karfe 2:45 na rana, wasu jami’an ƴan sanda su ka tare shi a Soliki, Aguda, Legas domin bincikar sa.

Oluwagbadura ya ce da misalin karfe 3:44 na rana, sai jami’an su ka tisa keyarsa har zuwa wajen mai na urar cirar kuɗi ta POS tare da cire masa kudi N100,000 daga asusunsa.

Ya ce bayan binciken da su ka yi ba su gano komai a kansa ba, sai su ka kwace wayar sa da kwamfutar tafi-da-gidanka ta kamfanin su, sai su ka yi masa kazafin shi dan yahoo ne.

Sun yi barazanar harbi da kulle shi daga baya, sai suka kai shi caji-ofis, ƴan mitoci kadan, sannan su ka tilasta shii kan ya yarda cewa shi mai laifi ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: