Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da wani rahoto da ya nuna cewa maganin tari na kamfanin Maiden na kasar India shine yayi sanadiyar mutuwar yara 66 a kasar Gambiya.

WHO ta fitar da nauikan magunan tari guda hudu inda yi umarni da a daina amfani da su.
Shugaban hukumar duniya Tedros shine ya bayyana haka a Geneva inda ya ce magunguna guda hadu wadanda kamfanin Maiden Pharmaceutical yayi su.

ya ce magungunan sun hada da Promathezine Oral syrup da Kofexmalin Baby Cough syrup da kuma makoff baby cough syrup da magarip N Cold Syrup.

Sannan magugunan sun yadu a fadin kasashe musamanma kasashen Afrika ta yamma.
Kuma yin amfani a wadannan magunan zai haifar da ciwon koda da kisa musammama ga yara.
WHO ta ce ta shiga lamarin saboda wani rahoto da ta samu daga kasar Gambiya inda ake kara samun yawan masu cutar ciwon koda a fadin kasar tun daga watan Yuli.
Sannan ta ce bayan gwaji ta gano magungunan na dauke da wasu sinadarai da ba a yarda da su ba wadanda za su jawo matsalar ciwon ciki da amai da gudawa rashin fitsari ciwon kai da ma taba lafiya kwakwalwa ko ciwon koda kuma su kan iya kai wa ga mutuwa.