Akalla mutane 30 ne su ka rasa rayukan su a lokacin da wani jirgin ruwa yayi hadari a Jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne a garin Umunnankwo da ke cikin karamar hukumar Ogbaru ta Jihar.
Shugaban Kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Ogbaru Hon Pascol Aniegbuna shine ya bayyana faruwar lamarin.

Shugaban ya ce an kuɓutar da wasu fasinjojin da ke cikin jirgin da dama kuma su ka rasa rayukansu.

Ya ƙara da cewa jirgin kwale-kwalen yayi hadarin ne bayan ya taso daga Gadar Onukwu zuwa Kasuwar Nkwo Ogbakuba duk a Ogbaru.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa jirgin yana dauke ne da mutane 85 a lokacin da ya kife a ranar Juma’a.
Ya ce rahotanni wanda bana hukuma ba ya nuna tsakanin mutane 20 zuwa 30 ba a gansu ba.
Tsohon dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ogbaru Hon Victor Afam Ogene ya tabbatar da faruwar lamarin tare da nuna rashin jinjidadi sa a kai.