Wata babbar kotu da ke zamanta a Dutsen Jihar Jigawa ta yanke wa wani tsoho mai shekaru 60 a duniya hukuncin daurin rai da rai bisa kamashi da aikata fyade ga wata karamar yarinya mai shekaru tara a Jihar.

Alkalin kotun A.M Sambo shi ne wanda ya yanke hukunci a yayin zaman kotun da ya gudana a ranar Juma’a.
Alkalin ya kara da cewa laifin da tsohon ya aikata ya saba da sashe na 282 na dokar Penal Code na Jihar da aka samar a shekarar 2012 da ta gabata tare da yin hukunci a karkashin sashe na uku na kundin laifuffuka na Jihar.

Alkalin ya ce tsohon ya yiwa yarinyar fyaden ne a gidansa da ke garin Dora cikin karamar hukumar Jahun ta Jihar.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa dashi.
A yayin shari’ar lauyan gwamnati ya gabatar wa da kotun shaidu tare da hujjoji guda biyu da su ka hada bayanin jami’an lafiya da kuma na jami’an tsaron ‘yan sanda.