Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mutum dan shekara 40 da ya hallaka wani jariri a kauyen Kadamti a karamar hukumar Numan ta Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Sulaiman Yahya Nguroje ne tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin ya hallaka jaririn ne bayan an kai wa mahaifiyar yaron hari.

Nguroje ya kara da cewa mahaifiyar yaron ta samu jikkata a yayin wani hari tun a ranar 9 ga watan Satumba 2022 a yankin Kadamati.

Kakakin ya ce jami’an da ke aiki a sashen Numan da mafarauta da sauran mutanen gari ne su ka samu nasarar kamo mutumin.

Nguroje ya bayyana cewa mutumin dan asalin ƙauyen Kpasham a karamar hukumar Demsa an kamashi sakamakon bayanan sirri da su ka samu.

Sulaiman Nguroje ya ce sun kwace kwari da baka, Wuka Kibiya da wasu manyan makamai a gurin wanda ake tuhuma.

Sannan ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar dashi a gaban kotu domin yi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: