A yau Lahadi marigayi Alhaji Muhammad Aminu Adamu Abba Boss ke cika shekara guda da rasuwa.

Kafin rasuwarsa, ya kasance mutum mai taimakon marayu, tausayin na ƙasa tare da jajircewa wajen ganin an tsaftace harkokin shugabanci a Najeriya.

Mutane sun yi masa shaida a kan abubuwan da su ka shafi cika alƙawari, kula da lokaci, girmama ɗan’adam da taimakon na ƙasa.

Ya kan ɗauki nauyin shirye-shirye domin jan hankalin gwamnati wajen ganin an sassautawa talaka musamman a kan halin tsadar rayuwa da ake ciki tare da tabbatar da mai mulki ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Marigayin ya rasu a ranar 09 ga watan Octoban shekarar 2021 a wani asibiti da ke Kano bayan jinyar da ya yi ta wani lokaci.

Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss, shugaban kamfanin gidan gonar Nana Farms LTD ya kasance guda cikin masu ɗaukar nauyin shirye-shirye a Mujallar Matashiya.

Kafin rasuwarsa ya fito takarar wakilcin ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano, wanda ya shiga jam’iyyun kamar PDP da APC.

Watanni kaɗan bayan rasuwarsa ƙanwarsa  ta rasu bayan gajeriyar jinya, haka kuma ƙasa da watanni uku mahaifiyar Abba Boss ta rasu.

Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa maza da mata har ma da jikoki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: