Babban sufeton ‘yan sanda a Najeirya Usman Baba-Alkali, ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da su bar ‘yan sanda su kula da sha’anin tallan ƴan takara na zaben 2023.

Alkali Baba, ya yi wannan kiran a ranar Lahadin da ta gabata a Maiduguri yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce an dauki matakin ne domin dakile duk wata karya doka da oda.
Ya ce suna so su roki ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa da su ba su damar daidaita jerin gwano da gangaminsu na yakin neman zabe don kada a yi karo da juna.

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa sai an nemi izini kafin a yi kamfen ko gangami domin ya sani ya ba da tsaro wurin yakin neman zabe ko kuma ya gayawa mutane ko wata jam’iyya ita ma tana kamfen a lokacin sai a bai wa jam’iyyar wani lokacin.

Yayin da yake tabbatar da kudurin rundunar na tabbatar da tsaro a zaben, Alƙali Baba ya ce ba za a amince da amfani da jami’an tsaro na bogi da kowane dan siyasa ko jam’iyya ya yi ba.
Ya nanata bukatar gudanar da aikin ‘yan sandan al’umma domin samun sakamako mai yawa na daƙile yunƙurin masu aikata laifuka, inda ya kara da cewa ‘yan sanda 10,000 da rundunar ta dauka a baya an tura su zuwa kananan hukumominsu daban-daban domin inganta aikin ‘yan sanda.
Sannan ya yi jinjina ga irin rawar da Civilian Joint Task Force, CJTF ta taka, a daidai lokacin da jami’an ‘yan sandan jihar Borno suka taka rawar gani wajen fallasa masu tada kayar baya.
Baba-Alkali ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Borno inda ya kaddamar da wasu ayyukan ‘yan sanda a Beneshiek da Maiduguri.