Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara.

An sace basaraken mai suna Marafa Danbaba da misalin karfe 1:45 na rana a gidansa da ke karamar hukumar Gummi bayan sun farmaki kauyen a ranar Lahadi.

A cewar wasu da abin ya faru kan gabansu, maharan sun ajiye baburansu a cikin daji kafin su taka zuwa kauyen sannan suka nufi gidansa.

Matsalar rashin tsaro a Zamfara na ci gaba duk da agajin da rundunar tsaro daban-daban ke kaiwa.

A ranar Asabar, an sake kai wani hari a kauyen Msama-Mudi da ke makwabtaka da karamar hukumar Bukkuyum.

A yayin farmakin, maharan sun nemi wani manomi da suka samu yana hutawa a karkashin bishiya da ya nuna masu gidajen masu kudi a garin.

Sauran mutanen da aka sace a harin sun hada da masu jego takwas da wasu matasa maza guda hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: