Gwamnatin tarayya zata kashe Naira Biliyan daya da miliyan dari daya, wajen gudanar da shari’u, da kuma hukunta masu tayar da kayar baya na Bokoharam.

Jaridar Sahara ta ruwaito cewa, hakan na kunshe ne cikin kasafin kudi da aka warewa ma’aikatar shari’a ta kasa na shekarar 2023.
Hakan na zuwa ne, dai-dai lokacin da babban attoni janar na kasa, a Juma’ar da ta gabata, ya bayar da umarnin sakin mambobin kungiyar boko-haram daga gidan gyaran hali na Kiri-kiri, saboda yafiya da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi musu.

Haka zalika, an ruwaito cewa, cikin kasafin kudin shekarar 2023, an warewa ma’aikatar ta shari’a sama da Naira biliyan biyu, domin gudanar da ayyukan shari’a daban-daban.
