Gwamantiin tarayayar Najeriya ta bayyana cewa ta hana amfani da wasu magungun wadanda suke hallaka Yara a fadin kasar.

Hukumar dake kula da ingancin abinci ta kasa NAFDAC ita ta bayyana haka ne inda ta ce ta haramata yin amfani da magunguna.

Cikin sanarwan da hukumar dake tabbatar da ingancin lafiya abinci NAFDAC ta ce duk wanda ya san yayi amfani da maganin promothezine Oral Solution da kofexmillan baby Cough syrup da kuma makoff baby cough syrup da magrip N cold syrup ya garzaya ya sanar da hukumomin lafiya.

Hukumar lafiya ta duniya ta haramta amfani da magungunan wadanda kamafanin maiden na kasar Indiya wanda aka bayyan cewa magungunan na dauke da cutarwa.

Daga cikin cuttukan da ake zargin magugunan sun hada ciwon kai amai da gudawa da ciwon koda.

Maganin tarin wanda ya hallaka yara akalla 66 a kasar Gambiya tun bayan fara amfani da magungunan.

Sannan kasar Gambiya ta janye yin amfani da magungunan.

Kuma hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ba iya kasar Gambiya ba ce ta yi amfani fa shi ba a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: