Wani rahoto na nuna cewa an fara yi wa mutanen Jamhuriyar Nijar mazauna Najeriya rajistar katin zabe a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba a yau Litinin.

Acewar mutane biyu ne masu yin rajistar, karkashin jagorancin Adamou Amadou za su shafe mako biyu a jihar domin su yi aikin rajistar.
Adamou Amadou, jagoran tawagar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, an turo su ne daga Ofishin Jakdancin Jamhuriyar Nijar da ke Abuja zuwa Kuros Riba domin suyiwa ’yan asalin Jamhuriyar Nijar rajistar katin zabe.

Sannan ya sanar da cewa, za su shafe mako biyu su na yin rajistar kuma duk inda dan Nijar yake ya samu labarin za su zo domin aikin.

Jami’in ya bayyana cewa idan suka kammala da Jihar Kuros Riba za su tafi garin Uyo na Jihar Akwa Ibom domin suci gaba da yin aikin a can.
Shugaban Kungiyar Kasar ’Yan Nijar mazauna Kuros Riba, Nasiru Ishaqa, ya bayyana matakin da gwamnatin kasarsu ta dauka na turo wakilai a yi musu rajista da cewa abin farin ciki ne, abin a yaba ne.