Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba za su bari wata jam’iyyar ta ƙwace mulki daga hannunsu ba don kada su mayar da Najeriya baya daga manyan ayyukan da su ka yi tsawon shekaru.

Muhamadu Buhari ya bayyana haka ne yayin buɗe yaƙin neman zaben shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a Abuja.
Ya ce a sakamakon hakan zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin ya jagorancin yaƙin neman zaɓen ɗn takarar shugaban ƙasa a jam;iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

Shugaba Buhari ya sha alwashin tabbatar da an ci gaba dga inda ya tsaya a mulkinsa domin kada a mayar da ƙasar baya.

Haka kuma ya buƙaci dukkan mambobin jam’iyyar da su tabbatar sun yi aikin da ya dace don ganin sun samu nasara.
Kuma ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC na da ingancin da zai jagoranci ƙasar don ganin an samar da cigaba mai yawa.