Rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata da masaniya kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yi a Najeriya game da yuwuwar kai hari babban birnin tarayya Abuja.

Da yake bayani ga tambayar da manema labarai sukayi masa a jiya Lahadi, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ba su da masaniya kan kowacce barazana na tsaro.

Da aka tambaye shi game da shirin yan sanda na dakile harin, kakakin rundunar wanda bai zurfafa magana kan lamarin ba, ya amsa tambayar a takaice da yace bashi da masaniya.

A halin da ake ciki, rundunar tsaro ta DSS ma ta ki cewa uffan ko amsa sakon da aka aike musu kan gargadin tsaron na jiya.

A ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba ne gwamnatin Amurka ta gargadi ‘ya’yan kasarta mazauna Najeriya kan tsaro, inda ta ce akwai yiwuwar samun hare-hare a wuraren taron jama’a a Abuja.

Sanarwar ta ce ana iya kai hare-haren ne a kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da shagunan siyayya, otal, mashaya, gidajen cin abinci da na wasanni har kan jami’an tsaro da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: