Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta kama wasu mata biyu da wasu maza biyu da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsu da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Ana zargin mutanen da safarar kayan maye sama da kilogiram 16,000 da aka kama a Legas da Abuja.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce a Legas jami’an yaki da muggan kwayoyi sun shafe makonni suna bin diddigin, Aro Aderinde mai shekaru 48, sun kama shi a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba, bisa zarginsa da hannu wajen fitar da tabar wiwi kilogiram 3,149 da aka boye a cikin kwakwa.

Haka kuma, an kama wasu mata biyu, Hauwa Bashiru da Basirat Adebisi Yahaya kan yunkurin fitar da kilogiram 90 na methamphetamine zuwa kasashen waje ta hannun Fasto Anietie Okon Effiong na Cocin Promise of Zion Church, Oron, jihar Akwa Ibom.

A baya anji cewa tun farko an kama Fasto Effiong a ranar Asabar 6 ga Agusta, 2022.

Wani da ake zargi da laifin safarar miyagun kwayoyi, Abdulkadir Mohammed, mai shekaru 47, wanda ake nema ruwa a jallo bisa kama shi da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5,640 a wani dakin ajiya da ke unguwar Chukuku a Kuje, Abuja, a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba, bayan kama matarsa, Saadatu Abdullahi, mai shekaru 35, wadda ta kasance an same shi a kanti lokacin da aka kai samamen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: