Rundunar sojojin saman Najeriya ta yi luguden wuta a kan mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP inda ta kashe gomman yan ta’adda.

A cewar Zagazola Makama, wani mai sharhi da ya karkata ga yankin Tafkin Chadi, ya ce yan ta’addan na jerin gwano ne lokacin da rundunar sojij sama ta farmake su.
Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi yayin da yan ta’addan ke jerin gwano tsakanin Shettima Abbor da Galmasku a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Rahoton ya kuma ce jirgin yakin rundunar sojin sama da aka kawo kwanan nan ne ya kashe mayaƙa.

Jaridar TheCable ta ruwaito daga majiya cewa an aiwatar da harin ne bayan bincike da aka gudanar ya nuno motoci biyu da babura da dama da yan ta’addan ke haye a kai.
Majiyar ta bayyana cewa jiragen yakin da aka tura don aikin ya yi jefa bama-bamai a kan ayarin motocin yan ta’addan inda ya lalata motar hilux daya tare da kashe mutanen da ke ciki.
Majiyar ta kuma kara da cewa rundunar soji da ke aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki za su ci gaba da kokarinsu na shafe da yan ta’adda da sauran miyagu daga yankin arewa maso gabas.
