Gwamnatin tarayya tace gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Kano da ake yi ya tsaya a dalilin barazanar da ake fuskanta na rashin tsaro a hanyar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda karamin Ministan ayyuka da gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub yana mai wannan bayani yayin da ya duba wani aikin titi a Kaduna.
Umar Ibrahim El-Yakub yace an tsayar da aikin bayan harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, aka yi gaba da wasu fasinjoji.

Rahoton yace Ministan ya fitar da jawabi a karshen makon da ya gabata ta bakin Daraktar yada labarai da hulda da jama’a, Blessing Lere-Adams.

Blessing Lere-Adams tace akasin abin da mutane ke fada cewa an yi watsi da aikin, ba haka lamarin yake ba, an dakata da aikin ne kuma za a cigaba.
Daraktar tace ba da dadewa ba za a cigaba da aikin titin na Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano domin an samu tsaro a yanzu.
A cewar Umar Ibrahim El-Yakub, aikin ya kai matakin da za a yaba, ya tabbatar da cewa ‘yan kwangila za su kammala ginin titin a lokacin da aka tsara.
