Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta tabbatar da yunƙurin kai wasu hare-hare a ƙasar bayan da gwamnatin Amuruka ta fallasa yunƙurin.

Jami’an sun yi kira ga ƴan ƙasar da su sake lura tare da kwantar da hankalinsu a kan lamarin.

Sanarwar da hukumar DSS ta sake tabbatarwa ta ce akwai yuwuwar kai wasu hare-hare a Abuja da wasu masu tayar da ƙayar baya ke shirin kaiwa.

Sanarwar ta ce yunƙurin da ake na kai hari masu tayar da ƙayar bayan za su kai ne zuwa gine-gine na gwamnati, wuraren cin abinci, gidajen giya,manyan kantuna da wuraren ibada.

Sauran wuraren da ake yunƙurin kai hare-haren su ne makarantu, kasuwanni, ma’aikatun ƙasashen waje da otel-otel.

Tuni ofishin jakadancin amuruka a Najeriya ya gargaɗi ƴan Amuruka mazauna Najeriya da su taƙaita tafiye-tafiye da zuwa wuraren da bai zama tilas ba.

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci jama’a da su ci gaba da lura tare da kwantar da hankalinsu domin au na aiki da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: