Gwamnatin jihar Anambra ta soke haraji da ake karɓa daga masu talla, masu tura kura da sauran kananan sana o’i a jihar.

Gwamnan jihar Farfesa Charles Soludo shine ya bada umarnin soke duk wani haraji da aka sanyawa ‘yan talla masu tura kura da sauran sana’o in hannu a jihar.

Gwamna Soludo ya bada umarnin ne lokacin da yake jawabi ga al’umar jihar kashi na biyu na taron yin nazari kan hanyoyin kudaden shiga Wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar dake Awka.

Farfesa Soludo yace ‘yan talla masu tura kura da makaneza ba za su biya haraji ba a jihar, Gwamnan ya kuma jaddada cewa dolene sakon ya shiga dukkan kasuwannin jihar.

Ya ci gaba da cewa masu tura kura kada su biya ko sisi ga kowa haka suma masu makaneza dake aiki akan titunan jihar su daina biyan kudin haraji a fadin jihar.

Gwamnan ya kara da cewa akwai bukatar gwamnati ta yi waiwaye kan masu kananan sana o’i domin farfado da tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: