Gwamnatin Najeriya ta nuna ɓacin ranta game da jerin gargadin da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ke fitarwa kan barazanar kai hare-hare a wasu sassan kasar harma da Abuja.

A martanin da ta mayar ta bakin ministan yada labarai Lai Muhammad, ranar labara a Abuja.
Gwamnatin Najeriya ta ce mazauna Abuja da sauran yankunan kasar basa cikin hadari.
Lai Muhammad yace ya na mai tabbatar wa al’umar Najeriya dana kasashen waje mazauna Najeriya cewa jami’an tsaro na bakin kokarinsu kan matsalar tsaro.

Ya kara da cewa babu wata barazana, kana ba bukatar wani ya tayar da hankalinsa.

Ministan yace ba Najeriya ce kawai ke fama da matsalar tsaro ba ko wacce kasa nada nata irin matsalar tsaro da take fuskanta.
Inda ya kafa hujja a hare-hare da daidaikun ‘yan bindiga ke kewa a Amurka.Martanin na Lai Muhammad na zuwa ne bayan da a ranar laraba ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayar da umarnin kwashe wasu daga cikin ma’aikatansa daga kasar.