Gwamnatin Najeriya ta amince ta kulla yarjejeniya da wani kamfani a kasar koriya ta kudu, da zummar gyara matatar man fetur ta Kaduna dake Arewacin kasar.

Shugaban kamfanin manfetur na Najeriya NNPC Malam Mele Kyari shine ya sanya hannu a madadin gwamnatin Najeriya, yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar kasar ke halarta a koriya, bisa jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce nan gaba kadan za’a fara zagayen duba gyaran da za’ayi.

A karshen shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta ware fiye da dalar Amurka Biliyan daya don gyaran matatar mai dake birnin fatakwal, aikin da tace ana cigaba da yi.

Kazalika za’a ci gaba da irin wannan aiki a matatar mai ta garin Wari na jihar Delta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: